Tarihin Annabi Idris. ( AS )
ʾIdris ( Da Larabci: إدريس) tsohon annabi ne da aka ambata a cikin Alqur'ani, wanda Musulmi suka yi imani da cewa shine Annabi na uku bayan Seth. Shi ne annabi na biyu da aka ambata a cikin Alkur'ani.
Idris ya kasance mutumen kirki mai faffadar kirji yana magana da murya kasa-kasa. Ana kuma cewa dogo ne kuma kyakkyawa kuma ko da yaushe yana magana cikin nutsuwa. Annabi Idris ya kasance mai matukar sha’awar sani, yana yin tunani a kan fa’idar duniya da mahaliccinsa ya yi daga sama, da kasa, da wata, da taurari da gajimare.
Idris bawan Allah ne na gaskiya, don haka ne Allah ya zabe shi a matsayin Annabi kuma Manzo, kuma ya zabe shi a matsayin shugaba a kan ‘ya’yan Adam.
Abin da ya fara bayan mutuwar Shiat shi ne mutanen Kayinu sun rasa jagora kuma zunubi da ɓarna sun fara karuwa da sauri kuma suna yaduwa. Idris ya kasa jurewa kallon mutanensa suna fadawa tarkon shaidan. Don haka Allah ya umurci Annabi Idris ya yi kira da a yi jihadi (yaki mai tsarki) a kan gurbatattun mabiya Qabil (Kain) —Idris shi ne Annabi da Manzo na farko a tarihin Musulunci da ya yi Jihadi da fasadi.
Kuma kamar yadda Allah ya umarce shi, Idris ya tara rundunar mutane ya yi yaki da sunan Allah a kan azzalumai, suka yi nasara.
Me aka san Annabi Idris da shi?
Anuhu shine annabi Idris. Shi ne na farko a cikin ’ya’yan Adamu da aka ba annabta kuma shine ya fara rubutu da alkalami.
An siffanta shi a cikin Alkur’ani a matsayin “amintaccen” kuma mai “hakuri” sannan kuma Alkur’ani ya ce an daukaka shi zuwa ga matsayi babba.
ALLAH SUBHANAHU WA TA ALA YANA CEWA
وذكر في الكتاب إدريس إنه كان صدقاً نبينا ورفعناه مكا نا عليا
KUMA KA AMBACI ANNABI IDRIS (ALAIHISSALAM) A CIKIN LITTAFI HAƘIƘA SHI ANNABI NE MAI YAWAN GASGATAWA, KUMA MUKA ƊAUKAKA SHI A GURI MAƊAUKAKI
Annabi IDRIS ALAIHISSALAM sunan sa na asali wanda aka yanka masa rago dashi Shine, AKHNUKH, ɗan Yardu ɗan Mahala'ilu, ɗan Kainanu, ɗan Anushu, ɗan Shisu, ɗan Annabi Adam Alaihissalam.
Sannan an ambace shi ne da suna IDRIS sabo da yawan karatun littatafai da yake yi, kuma shine wanda ya fara fiƙe al'kalami, kuma shine wanda ya fara rubutu, kuma shi ne wanda ya fara rubuta littatafai wato (TA'ALIFI).
Kuma shine farkon wanda ya fara bincike a cikin ilimin taurari, da na lissafi, kuma shine ya fara ɗinki a duniya wato (sana'ar Tela) domin su mutanen wannan lokacin bargo ko mayafi suke yafawa,.
A lokacin da Annabi IDRIS ya bayyana sai ya sami zare da allura ya ɗinka riga ya saka, da mutane suka gani sai wannan riga ta basu sha'awa, sai suka dinga kawo masa mayafan su da bargunan su yana maida musu su riga,, domin a lokacin babu wanda ya iya ɗinka riga sai shi a duniya, sannan sai daga baya mutane suka dinga kwaikwayon sa, sannan shine wanda ya fara kera sikeli, wato ma'auni.
Kuma baya cin wani abu sai da kuɗin da ya samu na wajan sana'arsa, ita ce ɗinki,, (tela) Amma du da wannan sana'ar ta Annabi Idris bata hana shi zikirin Allah ba, hasalima, duk lokacin da zai soka allura sai ya ambaci sunan Allah hakanan idan zai zare ta, sannan idan wani abu ya shagaltar dashi bai ambaci Allah ba, a sa wata allurar to fa sai ya warware wannan ɗinkin gaba daya, ya sake wani wanda zai Ambaci sunan Allah gaba daya A cikin yin ɗinkin.
اللهم صل وسلم وبارك على سيدنا ونبينا وحبيبنا محمد وعلى آله وصحبه أجمعين وسلم تسليما كثيرا إلى يوم الدين
ALLAH SUBHANAHU WA TA ALA ya saukarwa Annabi IDRIS ALAIHISSALAM Abun karantawa guda 30.
A lokacin da Aka aiko shi ya zama manzo, sai Annabi IDRIS ya shagala da karanta wannan littatafai, babu dare babu rana, mafi yawa daga cikin lokacin sa, sabo da yawan karatun waɗannan littatafai ne da yake yi, sai mutanan sa suka sa masa suna IDRIS ma'ana (mai yawan karatu) sannan da wannan suna ne Ubangiji madaukakin sarki ya ambace shi a cikin al'qur'ani mai girma,
Sannan Ubangiji ya aiko Annabi IDRIS zuwa ga ƴaƴan Ƙabilar ɗaya daga cikin ɗan Annabi Adam Alaihissalam wanda ya kafurta suka zama suna bautawa gumakan nan guda 5 wanda Ubangiji Subhanahu wa ta ala, ya ambace su a cikin qur'ani mai girma,, sune
Wudda, Da Yagusu, da Ya'uƙa, da Nasara, da Suwa'a,
Hakanan Annabi IDRIS ALAIHISSALAM ya dinga kiran su izuwa bautar Ubangiji Subhanahu wa ta ala shi kaɗai ba tare da sun haɗashi da kowa ba.
اللهم صل وسلم وبارك على سيدنا ونبينا وحبيبنا محمد وعلى آله وصحبه أجمعين وسلم تسليما كثيرا إلى يوم الدين
Malam Ibn Ishaq ya ruwaito cewa shi ne mutum na farko da ya fara rubutu da alkalami kuma an haife shi ne a lokacin da Annabi Adamu ya cika shekara 308 a rayuwarsa. A cikin tafsirinsa aya ta 19:56-57, malamin tafsirin Ibn Kathir ya ruwaito cewa: “A cikin Tafiyar Dare, Annabi (SAW) ya wuce shi a sama ta hudu.
Alqur'ani
An ambaci Idris sau biyu a cikin Alkur’ani, inda aka bayyana shi a matsayin mutum mai hikima. A cikin sura ta 19 a cikin Alkur’ani, suratu Maryam, Allah yana cewa:
Kuma ka ambaci Idrĩs a cikin Littãfi cewa: Ya kasance mai gaskatãwa, kuma Annabi, kuma Muka ɗaukaka shi zuwa ga wani wuri maɗaukaki.
Daga baya, a cikin suratu ta 21, al-Anbiya , an sake yabon Idris:
Kuma (ka ambaci) Ismã'ĩla da Idrĩsa da Zul-kifli , 19 dukansu (maza) mãsu haƙuri.
Kuma Muka shigar da su a cikin rahamar Mu, kuma sun kasance daga sãlihai.
Copy from SALIA SICEY Facebook
Comments
Post a Comment