JININ AL'ADA
(JININ HAILA)
Wanan maudu’i ne mai rikitarwa ba ga ‘yan mata kadai ba har da manyan mata da suka saba haihuwa. A wasu lokutan matsalar rashin haihuwa na samo asali ne daga rashin fahimta kan abunda ya shafi yanayin jikin mace, kwanakin yin jinin al’adarta, kai ciki har da lokacin da a ke sakin kwanhaihuwar mace zuwa mahaifa (wato obulation) da kuma lokacin kyankyashewa ko yanda ake kyankyashewar.
HUKUNCIN JININ ALADA A MUSULUNCI 1
https://sautulshifah.blogspot.com/2021/07/menene-jinin-alaada-haila.html
Galibin mutane sun san lokacin jinin haila wanda mace ke yi a kowane wata, sai dai kalilan ne kawai suka fahimci lokacin da a ke sakin kwanhaihuwa da kyankyashewa. A wanan rubutun zamu san minene jinin haila, lokacin sakin kwai, kwanakin da jinin ke yi, kai har ma da yanda mai jinin za ta dinga kula da tsabtace kan ta.
Menene Jinin Al’ada (Haila)
Jinin al’ada (jinin haila) wani jini ne na al’ada, wanda yake fita daga gaban (al’aurar) mace a kowane wata. Shi wannan jini a kimiyan ce ba cuta ba ne ko alamar cuta. Alama ce da take nuna ce wa, mace za ta iya daukar ciki (juna biyu). Ma’ana dai duk macen da take jinin haila, to tana cikin shekarun da mace ta ke daukan ciki. Fara jinin haila ga yarinya yana nuna jikinta ya fara kosawa za ta iya daukar ciki
HUKUNCIN JININ ALADA A MUSULUNCI 2
👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼
https://sautulshifah.blogspot.com/2021/07/jinin-alada-2.html
ta na yanzu shi ne ganin al’adarta na farko a rayuwarta, to abinda ya dace a kanta za ta zuba idone ta ga kwanaki nawa zai dauka kafin ya yanke, ta yadda ba zai wuce kwanaki sha-biyar ba, idan ko ya wuce sha-biyar to abinda ya doru akan kwanaki sha-biyar bai zama al’ada ba, kenan mafi yawan kwanakin da za ta saurara su ne kwanaki sha-biyar, amma zai iya daukewa kafin hakan, abin nufi in ya wuce to ya zama (Istihada) jinin cuta kenan, sai a nemi magani. Iyaye su saka ido akan ‘ya’yansu mata su dunga tuntubar su suna fahimtar da su tun kafin lokacin ya yi domin kada lokaci ya yi yarinya ta ga jini ta fashe da kuka, ko makamantan haka.
HUKUNCIN JININ ALADA A MUSULUNCI 3
👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼
https://sautulshifah.blogspot.com/2021/07/jinin-ala-ada-3.html
Wacce Ta Saba: Abinda ake nufi da wacce ta saba ita ce wace ta gabatar da al’ada sau uku a adadin kwanaki guda, misali wacce ta yi al’adar farko a kwanaki biyar, da ta sake yi sai ya yi mata kwanaki biyar da ta yi na uku shima kwanaki biyar, to wannan sai muce sunan ta wacce ta saba domin ta saba akan kwanaki sanannu. Amma idan ta yi al’adar karo na farko kwanaki uku karo na biyu kuma kwanaki biyar karo na uku kwanaki shida to ba za’a kira wannan wacce ta saba ba, domin bata da tsayayyun kwanaki. Ita wacce ta saba wato wacce take da sanannun kwanakin al’ada to wadannan kwanakin su ne kwanakin al’adarta, idan kwanakin suka cika al’adar kuma ta dauke sai ta yi wanka ta ci gaba da gudanar da ibada, amma idan kwanakin suka cika al’adar kuma bata dauke ba sai ta kara kwanaki uku, haka za ta din ga kara kwanaki uku har kwanaki sha-biyar su cika
Comments
Post a Comment