JININ ALA' ADA 3

 LITTAFIN FIQHU DARASI NA SHIDA 

Daga Mal.Aminu Ibrahim Daurawa

IDAN  HAILA TA ZO  KWANA NAWA TAKE YI YADDA IDAN  TA WUCE WAƊANNAN KWANAKIN ZA A ƊAUKA BA HAILA BA CE?


Wannan mas’ala ita ma malamai sun yi saɓani a kanta, ta iyakance kwanakin da mace za ta yi ta daina al’ada, ko kuma iya kwanakin da ala’da za ta yi, idan ta wuce wannan kwanakin za a ɗauka cewa ta fita daga al’ada.

Malamai na farko suka ce babu iyaka dangane da ƙarancin kwanakin al’ada, ko kuma mafi yawansa. Duk lokacin da mace ta ga jini ko da kuwa awa ɗaya ne ko kwana ɗaya, ko da daddare, ko da rana, ko mafi yawa ko mafi qaranci, wannan haila ce, idan kuma ya ɗauke shi kenan ta  ɗauke.

Saboda haka, akan sami mata waɗansu suna yin al’ada kwana ɗaya kawai a wata, ko kwana biyu, ko uku a wata, ko biyar ko shida ko bakwai duk wata. Amma idan za ka tambayi mata dubu za ka samu cewa kusan kaso casa’in cikin ɗari za su ce ba sa wuce kwana shida ko bakwai, duk da wasu matan sukan wuce hakan. Wata takan yi kwana takwas, wata kwana tara, wata kwana goma kai har akwai masu yin kwana goma sha biyar. Kai har an sami mai yin kwana ashirin tana al’ada duk wata. Don haka a kowanne wata sai ta yi kwana ashirin tana zubar da jini, sannan ta yi kwana goma tana cikin tsarki.

Wata kuma rabi, duk wata za ta yi rabi, wato kenan akwai masu yin ɗaya bisa goman wata shi ne kwana uku. Akwai masu yin ɗaya bisa shidan wata suna yin jini shi ne kwana biyar, da masu yin ɗaya bisa huɗu na wata, shi ne sati guda suna jini, da masu yin biyu bisa uku na wata, wato kwana ashirin suna jinin al’ada . Haka Allah ﷻ Ya haliccesu; tun farawarsu haka suka fara kuma haka suke yi.

Saboda haka sai malamai suke ganin mafi ƙaranci ya kamata a yi masa iyaka tun da ba a sami hadisi ko aya da ta yiwa jinin al’ada iyaka ba dangane da mafi ƙarancinsa, ko kuma ta yi masa iyaka dangane da mafi yawansa. Wannan ya sa malamai suka yi saɓani wajen iyakance yawansa, kuma wannan ya ginu ne a kan bincike da tambayoyi da suka yi wa mata saboda a cikin malaman babu mai yin jinin al’ada ko mutum ɗaya. Don haka sun gina ne a kan tambayar matan da suke yin jinin al’ada, da kuma dogaro da suka yi a kan wasu nassoshin.

Saboda haka kowa a yankinsa sai ya tara mata da suke yankin ya tambaye su yaya jinin al’ada yake a tsakaninsu? Wata ta ce, malam ni kwana goma nake yi, wata ta ce kwana biyar take yi. Idan ya bincika ya samu a cikin mata dubu an sami xari takwas suka ce suna yin kwana shida, sai malam ya ɗauka cewa kwana shida shi ne mafi yawa, kuma shi ne abin da za a gina hukunci a kai. Ko kuma ya bincika mata dubu biyu ko dubu uku duk amsarsu ta zamo cewa babu wacce take wuce kwana goma sha biyar (15) sai malam ya ɗauka cewa, tun da dai an sami mace xaya a cikin dubu ita ce kaɗai take kaiwa kwana goma sha biyar, sai a ɗauka mafi tsawonsa shi ne kwana  goma sha biyar. Don haka duk wannan iyaka da malamai suke yiwa jinin al’ada da kwana ɗaya ko biyu ko uku ko huɗu ko biyar ko sha biyar, ko idan ya wuce sha biyar ya zama ciwo, an gina shi ne a kan bincike da tambayoyi da ake yiwa mata da fahimta da ijtihadi, amma ba Allah ﷻ ko Annabinsa ﷺ ne suka iyakance shi a cikin aya ko hadisi ba. Waɗannan kwanaki duk bincike ne da ijtihadi na manyan malamai, Allah ﷻ Ya saka musu da alheri. Saboda haka ake samun bambance-bambance tsakanin fatawoyi da abin da ake faɗa da kuma abin da su matan suke yi. 

Saboda haka a taƙaice, haila ba ta da mafi ƙarancin kwanaki ta yadda za a ce ƙasa da shi ba haila ba ce. Haka kuma ba ta da matsakaitan kwanaki ta yadda za a ce sama da shi ba haila ba ne. Amma idan a gaba ɗaya watan jini yake zuba, an san kuma babu wata mata da za a ce kwana talatin take yin haila, ma’ana duk wata sai ta yi kwana talatin don haka kenan a shekara za ta yi kwana ɗari uku da kusan hamsin da shida tana yin jinin al’ada, wannan ka ga kenan jinin ma ba ya tsayawa kwata-kwata, ita wannan hukuncin ta daban. Za a yi bayanin wata mata da tai shekara shida a zamanin Annabi ﷺ jini yana zubar mata ba ya ɗaukewa, kuma ta je ta tambayi Annabi ﷺ a kan haka kuma ya ba ta mafita ta hanyar mayar da ita zuwa ga mafi yawan abin da mata suke yi na al’ada, shi ne kwana shida ko bakwai. An kasa matan zuwa kashi uku wanda za mu ji kowacce da bambance-bambancen da yake tsakanin su.

Saboda haka kenan a taƙaice, haila takan iya zama kwanaki kaɗan, kuma takan iya zama kwanaki da yawa. Matuqar jinin bai zarce da zuba har ƙarshen wata ba, za a yi masa hukunci a matsayin haila ne, sai idan mace za ta iya bambance kalar jinin haila da wanda ba na haila ba, kuma tana da al’adarta sananniya daga baya abin ya zo ya rikice mata ya qaru, sai ta koma kan al’adarta. 

A nan mata sun kasu kashi huɗu:

1. Akwai macen da tana da al’adarta sananniya. Misali, kwana shida take yi sai jini ya zo ya rikice mata ya qaru akan kwana shidan. Wannan sai ta koma kan al’adarta idan jini ya wuce qa’ida ta dinga lissafin kwanakin da take yi a baya.

2. Akwai matar da ba ta da al’ada sananniya, ko kwanaki sanannu, amma kuma tana iya bambamce kalar jinin hailar da wanda ba na hailar ba. Wannan sai ta yi amfani da wannan ilimi da take da shi na bambance jini. Da zarar ta ga jinin ya sauya, ta san yanzu ba na al’ada ba ne. Sai ta yi wanka ta ci gaba da sallah.

3. Wacce take tana da al’ada sananniya kuma tana iya bambance kalar jinin ko launinsa, sai ta yi amfani da al’adarta da bambance kalar jinin. Idan jinin ya sauya ya fita daga na al’ada ya koma na ciwo sai ta yi amfani da wannan basira da ilimi da Allah ﷻ  Ya ba ta.

4. Wadda ba ta da al’ada sananniya, ko wasu kwanaki sanannu tun lokacin da aka haife ta, ko kuma ba ta iya bambance kalar jinin ba, sai ta koma mafi yawan abin da mata suke yi, shi ne kwana shida ko kwana bakwai. Duk wata idan kwana shida ya wuce sai ta yi wanka ta ci gaba da yin sallah, sai kuma wani watan. Haka za ta ci gaba da yi domin shi ne iya abin da za ta iya. Masu wannan magana sun kafa hujja da faxin Allah ﷻ cewa:

﴿ وَيَسْأَلُونَكَ عَنِ المَحِيضِ قُلْ هُوَ أّذًي فَاعْتَزِلُوا النِّسَاءَ فِي المَحِيضِ وَلاَتَقْرَبُوا هُنَّ حَتَّى يَطْهُرْنَ ﴾ ()

Ma’ana: “Suna tambayar ka game da haila, ka ce cuta ne, wato qazanta ne, ku nisanci mata lokacin da suke jinin al’ada, (ku nisanci saduwa da su idan suna cikin jinin ala’da)  har sai sun sami tsarki.”

Na ɗaya, a nan Allah ﷻ Ya alaƙanta nisantar mata a bisa samuwar jinin. Don haka duk lokacin da aka sami wannan jini, kwana xaya ne ko biyu, da daddare ko da rana, mafi qaranci daga kwana ɗaya ne ko mafi yawa daga kwana ɗaya, wajibi ne mutum ya nisanci matarsa. Don haka sai ya nuna cewa, hukuncin haila an gina shi ne a kan samuwar jinin, ba a kan yawan kwanakin ko ƙarancin su ba.

Na biyu, hadisin Nana Ai’shah (رضي الله عنها) da Manzon Allah ﷺ Ya ce: “Idan hailarki ta gabato, to ki daina sallah, idan ta ba da baya ki wanke jinin ki yi sallah.”

 A nan ma Annabi ﷺ ya gina hukuncin jinin al’ada ne a kan  zuwansa  ko ɗaukewarsa ba tare da la’akari da wasu kwanaki sanannu ba.

Na uku, hadisin Nana A’ishah (رضي الله عنها) lokacin da ta yi jinin al’ada suna tare da Annabi ﷺ a lokacin Hajji, sai Annabi ﷺ ya ce: “Ki aikata abin da mai aikin Hajji yake aikatawa sai dai ba za ki yi ɗawafi da Xakin Allah ﷻ ba, sai kin yi tsarki.” 

A nan ma, Annabi ﷺ ya gina hukuncin jinin al’ada bisa samuwarsa, ba tare da sa wani lokaci sananne ba.

Sai dai idan mace ta ga jini ya zo qasa da kwanakin da ta saba yi na al’ada, ko kuma ya wuce wannan lokacin, a nan me ya kamata ta yi?

Ya kamata ta yi la’akari ta duba da kyau zai iya kasancewa hailar ne ya qaru. Zai iya kasancewa ba jinin hailar ba ne na cuta ne, ko kuma jini ne na rashin lafiya. Saboda haka, a nan sai ta yi bincike ta hanyar duba kalar jinin ko kuma duba al’adar da take yi kafin ta sami wannan lalura, domin mafi yawan mata suna yin kwana shida ne ko bakwai suna jinin al’ada, kamar yadda ya zo a hadisin Amratu bint Jahsh, Annabi ﷺ ya ce: “Ki yi jinin al’adarki a bisa ilimin Allah ﷻ kwana shida ko bakwai shi ne na mafi yawa ga mata, sannan ki wanke, ki yi wanka, ki sallaci kwana ashirin da huxu, ko kuma kwana ashirin da uku, idan kin xauki kwana bakwai za ki dinga yi duk wata, saboda jini yana zubar miki kullum sai ki mayar da shi kwana shida ba kya yin sallah. Bayan kwana shida sun wuce, sai ki yi wanka ki ci gaba da yin sallah. Kin ga a lokacin kin yi kwana ashirin da uku kenan kina yin sallah a watan. Kuma idan kin ɗauki kwana shida kin ga kenan za ki yi kwana ashirin da huɗu kina yin sallah, kwana shida kuma ba kya yin sallah, gwargwadon yadda mafi yawan mata suke yi.”

2-

Daga  sheikh Aminu Ibrahim daurawa 

TSAKANIN JININ HAILA ZUWA WANI JININ HAILAR, KWANA NAWA A KE SAMU MAFI YAWA?

Wato idan mace ta yi jini ya ɗauke, zuwa kwana nawa ne za a ce sabon jini ya zo ko kuma zuwa kwana nawa ne za a ce a’a wancan jinin na baya ne ya ci gaba da zuba?

A nan shi ma malamai sun yi tattaunawa ta ilimi wajen tantance kwanakin da tsakaninsu ne za a ce an shiga sabuwar haila?

Wasu sun ce sai ya kai kwana takwas. Idan mace ta yi jini ya ɗauke bayan kwana takwas idan wani jinin ya zo, to wannan sabon jinin haila ne ba wancan na baya ne ya ci gaba ba.

Wasu suka ce, a’a idan an sami kwana goma a tsakani, mace ta yi jinin al’ada ya ɗauke ta yi wanka tana sallah, bayan kwana goma sai jini ya zo wannan wani sabon jini ne ya zo.

Wasu suka ce, a’a sai an sami kwana goma sha biyar a tsakaninsu, idan mace ta yi tsarki sai bayan kwana goma sha biyar idan wani jinin ya zo sannan za a ce ga sabon jinin haila nan ya zo. Amma idan kafin waɗancan kwanakin ne sai a ce wancan na biyun ne ya ci gaba da zuwa. Saboda haka da wannan jinin da ta yi na farko da wannan na biyun duk za a ɗauke su a matsayin jini guda ɗaya. Wannan shi ne abin da wasu malaman suka faɗa.

Wasu malaman kuma suka ce, wasu sashin mata sukan tsarkaka daga hailarsu, sannan jini ya dawo musu karo na biyu, wanda bai wuce tsakanin su kwana goma ko kwana goma sha biyar ba, za a ɗauki wannan jinin na biyu a matsayin haila ne ko kuma jinin baya ne ya ɗoru, wato ba sabuwar haila ba ce, waccan ce ta ci gaba? Akwai saɓanin malamai da yawa, amma abin da ya fi shahara shi ne, mafi ƙarancin tsarki tsakanin haila guda biyu shi ne, kwana goma sha biyar ko goma sha uku. Don haka, idan mace ta sami tsarki daga hailarta, sannan sai jini ya sake dawo mata karo na biyu kafin cikar kwana goma sha uku ko sha biyar, ba za ta gina hukuncin a kan cewa haila sabuwa ta zo ba, sai dai ta ɗauka a kan cewa wancan jinin ne na baya ya dawo ko kuma jini ne na ciwo ya dawo mata.

Wasu kuma daga cikin ma’abota ilimi sun ce, babu iyaka tsakanin jinin al’ada guda biyu. Wato idan jini ya zowa mace bayan ta yi tsarki, bayan wasu kwanaki kuma sai jini ya dawo, sai a ce ta shiga haila ta biyu.

Kamar matar da aka sake ta, sai ta yi haila ta kwana shida yadda ta saba, amma bayan kwana biyar sai wani jinin ya dawo, za ta iya cewa ta shiga jini na biyu, kuma bayan kwana biyar sai wani jinin ya dawo, za ta iya cewa ta shiga jini na uku. Za ta iya cewa ta gama iddarta a wata ɗaya, tsakanin kowanne jini a sami ‘yan kwanaki. Wanda kuma a baya mun ce akwai malaman da suka ce, jini sai ya kai kwana goma, ko kwana takwas, ko kwana goma sha biyar wanda shi ne ya fi shahara a tsakanin malamai. 

Sun sake kafa hujja dai da ayar nan ta cikin Suratul Baqara (wadda ta ce, “Kuma suna tambayar ka game da jinin haila na mata, ka ce wannan qazanta ne, ku nisanci mata a lokacin da suke jinin al’ada kada ku sadu da su.” A nan Allah ﷻ Ya gina hukunci ne ba tare da ya iyakance wani lokaci na musamman ba . Wannan iyakance lokaci ya samu ne da ƙoƙarin malamai da ijtihadi domin su sauƙaƙawa mutane don su fi saurin fahimta, ba wai don cewa lallai wannan maganar sai an sami kwana kaza ba, maganar Allah ﷻ ce ko ta ManzonSa ﷺ. 

Sannan ya zo a hadisin Nana A’ishah (رضي الله عنها) ta ce, “Idan hailarki ta gabato, to ki daina sallah, idan ta ba da baya ta wuce sai ki wanke jinin ki yi sallah.” A nan, Annabi ﷺ ya gina hukuncin haila ne a kan zuwan jini, ba tare da tsayawa zuwa lokaci kaza ba.

Hujja ta uku, wannan ƙaddarawa da malamai suke yi da kwana kaza, duka babu abin da ya zo a cikin littafin Allah ﷻ ko a sunnar Manzon Allah ﷺ kuma da a ce lallai sai an yi la’akari da wannan za a gina hukunci, da Shari’a ta gina hukunci a kai, domin al’amarin jinin al’adar nan yana da alaƙa da manya-manyan ibadu, musamman sallah saboda idan ana jinin al’ada mace ba ta sallah da azumi.Yana da alaƙa da saki, domin ba a sakin mace idan tana jinin al’ada. Mace ba ta sallah ko azumi ko ɗawafi idan tana jinin al’ada. Babu abin da aka gina hukunce-hukunce a kansa irin wannan. Da waɗannan kwanaki da ake iyakancewa suna da muhimmancin gaske da Allah ﷻ da kanSa zai bayyana su a cikin Al-qur’ani mai Girma, ko kuma Manzon Allah ﷺ ya bayyana su a cikin hadisi. Amma saboda abu ne da ya shafi mata, matan nan kuma suna sassauyawa daga gari zuwa gari, ko ƙasa zuwa ƙasa, ko lokaci zuwa lokaci, ko yanayin jiki zuwa yanayin jiki, ko yanayin kwanciyar hankali ko damuwa, ko kuma irin abincin da ake ci, jinin nan yana ƙaruwa ko ya ragu. Don haka sai aka bar abin a bisa kowacce ta yi la’akari da abin da ta sami kanta a ciki. 


MENENE MAFI YAWAN KWANAKIN TSARKI GA MACE?

Babu iyaka dangane da mafi yawan kwanakin tsarki ga mace. Mace za ta iya gama jinin al’ada, kuma sai bayan wata zai zo. Ko ta gama jinin al’ada ba za ta sake yi ba sai bayan wata biyu, ko wata uku, ko shida, ko sai shekara-shekara take yin jinin haila. 

Don haka, idan aka sake ta sai ta yi shekara uku sannan za ta gama iddarta. Wata idan an sake ta sai ta yi shekara ɗaya. Wata kuma wata huɗu-huɗu ko wata uku ko wata tara kenan za ta gama iddarta. Saboda haka wannan ya danganta domin kowacce mace akwai yanayin jinin al’adarta. 

Akwai ma wadda ba ta yin hailar kwata-kwata a raywurta. Saboda haka wannan ya sa malamai suka ce tun da abin ya danganta da mata, ba za a iya yanke hukunci guda ɗaya ba, sai dai kowacce mace a tambaye ta, yaushe take yin jinin al’ada, kuma kwana nawa take yi, kuma idan ya ɗauke bayan kwana nawa, ko wata nawa, ko sati nawa, ko awa nawa, yake dawowa? Don haka kowacce za a gina mata hukuncinta ne a kan yadda aka same ta da kuma yanayin da ta sami kanta a ciki.


SHIN MACE MAI CIKI TANA YIN HAILA KO BA TA YI?

Malamai sun yi saɓani dangane da mai ciki cewa idan ta ga jini haila ne ko ba haila ba ne?

Malamai na farko, suka ce mai ciki ba ta yin jinin al’ada kwata-kwata. Saboda haka idan aka ɗauki wannan ƙaulin, (maganar) duk jinin da ya zowa mai ciki, jini ne na rashin lafiya ba zai hana ta ibada ba. Don haka za ta wanke wannan jini ta ci gaba da yin ibadarta kamar yadda ta saba. Kuma wannan shi ne abin da mafi yawan likitoci na duniya suka tafi a kai, kuma ita ce mazhabar Malam Abu Hanifa da Imamu Ahmad da wasu manyan malamai 

Na biyu, suka ce ana iya samun mace mai ciki ta yi jinin al’ada, duk da ba kasafai a kan samu ba, amma kowacce mas’ala akan sami abin da yake ya fita daban. Akan sami macen da ta fita daban a cikin mata, ga ta da ciki kuma tana al’ada. Sai dai a nan idan an sake ta ba za a yi la’akari da cewa sai ta yi jini uku ba. Tun da dai tana da ciki lallai sai ta haihu, don haka ba za a yi amfani da wannan al’adarta ba a wajen idda ba, sai dai a yi amfani da ita a wajen ibada. Abin nufi sai bayan wata uku ko bayan wata shida, idan ta ga jini yana fita yadda ya saba zuwa a lokacin al’ada da kalarsa da lokacinsa yadda ta saba, haka take da ciki ma tana al’ada. Wannan sai a yi mata hukunci da abin da ya bayyana daga ɗabi’arta da halinta. Saboda likitoci sun ce ba a yin haila idan mace tana da ciki, ga shi ita kuma ta yi ɗin. Amma fa da wuya a sami mace tana da ciki kuma tana yin haila. Idan kuwa an samu ɗin sai a yi mata hukunci da abin da ya bayyana a gare ta, domin ita ta bambanta da sauran mata: ga ciki ga al’ada. Ana samun ‘yan kaɗan mata masu yin wannan, amma dai asali shi ne, idan mace tana da ciki ba ta jinin haila.


IDAN JININ ALA’DA YA ƊAUKEWA MACE KAFIN LOKACIN AL’ADARTA YA CIKA, YA ZA TA YI?

Abin da malamai suka ce shi ne matuƙar dai jini ya ɗauke, mace ta je ta yi wanka ta ci gaba da sallah. Wataƙila yanzu daga kwana shida ya dawo kwana biyar, don haka ba za ta ce bari in jira sai kwana ɗayan nan ya cika ba. Matuqar ta duba jinin a lokacin kwanciya ko lokacin tashi ta ga alamar ɗaukewar jini, sai ta yi wanka ta ci gaba da sallah kuma ta ɗauka cewa kwanakin al’adarta ne suka ragu.


MACEN DA LOKACIN AL’ADARTA YA SAUYA YA ZA TA YI?

Ma’ana, lokacin ya sauya, kwanaki ba su ƙaru ba amma sai lokacin ya sauya ta daina yi a farko, ta koma ƙarshe ko kuma a ƙarshe take yi sai ta dawo baya, ko farko, wannan duka ba zai sauya hukuncinsa da cewa shi jinin al’ada ba ne. Saboda ayar da muka gabatar ta gina hukunci ne a kan jinin al’ada ba tare da cewa a farkon wata ko tsakiya ko ƙarshe ba. 

Haka a hadisin Nana A’ishah (رضي الله عنها) cewa Annabi ﷺ Ya ce: “Duk lokacin da kika ga jinin haila, to ki daina sallah.”   Bai ce ko a farko ko ƙarshe ba. Saboda haka, ya nuna duk lokacin da jini ya zowa mace, ko lokacin jinin ya sauya, ko adadin kwanakin suka ƙaru ko ragu, ko lokacin ya sauya ya yi gaba ko baya, duka wannan yana nan a jininsa na al’ada kuma za a gina hukunci ne a kan jinin da ɗaukewarsa, zuwansa, ƙaruwarsa da raguwarsa, kamar yadda malamai suka tabbatar da haka.


ƘARUWAR JINI A KAN NA AL’ADA

Shin idan mace ta saba yin haila kwana shida, sai kuma ya koma kwana bakwai ko kuma ta saba yin kwana bakwai sai ya koma kwana goma, ya za ta yi da wannan qarin kwanakin da ta samu na al’adarta? 

A nan ma akwai tattaunawa ta ilimi a tsakanin malamai, amma abin da ya fi rinjaye shi ne, wannan kwanaki da suka ƙaru, shi jinin al’adar ne ya ƙaru, don haka wannan kwanaki da suka qararwa mace na wucewa yadda ta saba al’ada ya qaru da kwana ɗaya ko biyu ko uku ko huɗu, malamai sun yi saɓani.

Wasu sun ce, wannan shi ma jinin al’ada ne, don haka sai ta bari bayan kwana uku sai ta yi wanka ta yi sallah, ko da jinin ya ci gaba da zuba. Wata na biyu ma idan ya zo shi ma haka za ta yi sai ta ƙara kwana uku a kan kwanakin wancan watan. A wata na gaba ma ta qara kwana uku, har ya kai kwana goma sha biyar. Daga nan duk abin da ya ƙaru a kan sha biyar ba jinin al’ada ba ne.

Wasu malaman suka ce, mace za ta yi la’akari da kalar jinin. Idan jinin nan da yake zuba irin na ala’da ne, da ɗabia’rsa da kalarsa da yanayinsa, to kawai za a ɗauka kwanakin al’adarta ne suka ƙaru. Saboda haka za ta yi amfani da cewa yanzu kwanakin al’adarta sun tashi daga kwana shida sun koma kwana goma. Saboda haka sai kwana goman ya cika jinin ya ɗauke sai ta yi sallah. Don haka sai suka kafa hujjoji guda uku:

Ayar da Allah ﷻ Yake cewa: “Suna tambayar ka game da mai al’ada, ka ce, wannan ƙazanta ne” (wato najasa ne). ()  A nan Allah ﷻ Ya gina hukunci ne a kan samuwar jinin ba wai kwana nawa yake yi ya ɗauke ba, ko kwana nawa yake ya zo, ko ya ƙaru ko ya ragu ba. Duk lokacin da aka sami wannan jini hukunci na nan. Saboda haka hukunci yana zagayawa ne tare da abin da aka gina hukuncin a kai, shi ne jinin al’ada. Idan ba jinin al’ada, ba hukunci, ba tare da lura da cewa kwana nawa ya yi ba.

An ruwaito daga Nana A’ishah (رضي الله عنها) cewa, “Idan hailarki ta gabato ki daina sallah. Idan ta ba da baya, ki wanke jinin, ki ci gaba da sallah.”  Suka ce, a nan Annabi ﷺ ya haɗa hukunci ne a kan samuwar jinin haila; zuwansa da ɗaukewarsa. 

Saboda haka idan mace ta sami kanta a kan kwanaki suna qaruwa gare ta, matuƙar jinin shi ne ba wai kalarsa ce ta sauya na ciwo ya zo ba. 

Idan kuwa ta tabbatar ko tana da zato mai qarfi cewa wannan jinin da ya ƙaru ba na al’ada ba ne, sai ta ginu a kan wannan zato nata mai ƙarfi ko yaƙini nata. Idan ya zo sai ta yi wanka ta yi sallah ta ɗauka wannan kwanakin da suka ƙaru rashin lafiya ce ba jinin haila ba ne. Allah ﷻ Shi ne mafi sani.

Zamu ci gaba insha Allah.

Comments