Na fito gaba gaɗi
Dakta Rabe ya firgita ni
Ta taho da littafa
Sai Kabiru ya hargitsa ni
Sai na dosa kwana da wayau
Babu wanda ya tallafa ni
An ka juya gun Maɗatai
Nan da nan ko ya jijjiga ni
Har da ma Masa'udu shi ma
Bai raga ba ya ƙarasa ni
Na ji kunya an ƙure ni
Gaskiya ta ƙaryata ni
An ƙure dukkan gudu na
Na ji kaye, na yi rauni
Yanzu an san ban da hujja
Ni yawan fahari gare ni
Can cikin yaran gidana
Nai ta surutu da sai ni
Nai ta cewa koda waye
Zan buga ni ban da rauni
Yau ko an zo an ritsa ni
Ga shi nan an lallasa ni
Nai ta zare ido da wayau
Sai zufa da ta lulluɓe ni
Har na ɗau robar ruwana
Ban sani ba na sha da hauni
Sai na ce ba lokaci ne
Babu adalci gare ni
Na sani ƙarya nake yi
Duniya ta kunyata ni
An yi min zindir a titi
Video ya sajjala ni
'Yan jaridu na ta cewa
Ya akai aka jijjiga ni?
Sai na ce musu ya kuke so
Na yi bayan an ƙure ni?
Yanzu kowa ya ga cewa
An gama, an murmusa ni
Ban da hujja ba karatu
Ni biɗar girma ya kai ni
-Tammat bihamdil Lah
Asgar2021
Comments
Post a Comment